An nada Hakimai na riko 32 a Adamawa


Majalisar Sarakunan jihar Adamawa ya sanar da naɗin sabbin hakimai 32 na riƙo.

Majalisar Sarakunan Jihar Adamawa, karkashin jagorancin Lamiɗon Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkinɗo Aliyu Mustapha, ta sanar da naɗin sabbin hakimai 32 a matsayin na riƙo.

Sanarwar naɗin ta fito ne ta hannun Kabiru Bakari, Tariya Adamawa, wanda ya sanya hannu a wata takarda da ta bayyana sunayen dagatan da aka naɗa.

A cewar sanarwar, an naɗa hakiman ne a sabbin yankunan da gwamnatin jihar ta ƙirƙira don kula da al’amuran sarauta da inganta mulkin gargajiya a yankunan.

Duk da haka, sanarwar ta bayyana cewa ba a ayyana sunayen hakiman riƙo na yankunan Murke da Sate ba, inda aka bayyana cewa za a sanar da su nan gaba.





Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *