Gwamnatin Kaduna ta mayarwa Iyalan Abacha filayensu da El-Rufai ya kwace


Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya mayar wa iyalan tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, filayensu guda biyu da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya ƙwace a zamanin mulkinsa.

Lauyan iyalan Abacha, Reuben Atabo, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Babban daraktan ma’aikatar kula da filaye ta Jihar Kaduna, Mustapha Haruna, ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya aika wasiƙa ga iyalan Abacha, inda aka tabbatar da mayar musu da filayen.

A cewar wasiƙar, an kuma buƙaci iyalan su biya harajin da ake karɓa sakamakon mallakar filayen.

Tun a ranar 28 ga Afrilu, 2022, tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya ƙwace filayen tare da soke mallakarsu, matakin da ya jawo cece-kuce a lokacin.

Gwamnan Uba Sani, a nasa bangaren, ya bayyana cewa matakin dawo da filayen na da nufin tabbatar da adalci ga kowa.





Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *