Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa babu gudu, babu ja da baya kan gyaran harajin da gwamnatinsa ta ƙaddamar kwanan nan, wanda ya haifar da cece-kuce.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi a hirar sa ta farko da kafafen yaɗa labarai a ranar Litinin da daddare, inda Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba zai yiwu a farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar da tsoffin tsare-tsare da suka gaza ba.
“Gyaran haraji ya zo domin ya zauna; ba za mu ci gaba da yin abin da muka saba yi shekaru da shekaru ba a cikin wannan sabon tattalin arzikin. Ba za mu iya sake farfaɗo da tattalin arzikin nan da tsoffin littattafan da suka lalace ba.
“Ina mayar da hankali kan abin da Najeriya ke buƙata da abin da dole ne na yi wa Najeriya. Ba zai zama sauƙi ga kowa ba, amma sabon salo ya zo.
“Ina da tabbacin cewa ina da ƙarfin da ake buƙata, shi ya sa na shiga wannan takara,” in ji Tinubu.
A ranar 3 ga Oktoba, Tinubu ya aika da kudirori huɗu na gyaran haraji zuwa Majalisar Ƙasa.
Wadannan kudirorin gyaran haraji sun haifar da cece-kuce tun bayan gabatar da su a Majalisar, inda suka fuskanci ƙalubale da adawa musamman daga yankin Arewancin ƙasar.