Kirsimeti: Gwamnati ta yi kyautar N20m ga Kiristoci a jihar Kano


Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya aikewa Kiristoci a jihar sakon taya murna yayin da suke bikin Kirsimeti na shekarar 2024.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, Yusuf ya bukaci Kiristoci su yi godiya ga Allah da ya ba su damar ganin wannan lokaci.

Ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Dawakin-Tofa, gwamnan ya bukaci Kiristoci da su rungumi mutunta juna da zaman lafiya yayin da suke bukukuwan.

“A yayin da kuke jin daɗin wannan lokaci, ina roƙonku da ku rungumi mutunta juna da zaman lafiya,” in ji Yusuf.

Gwamnan ya jaddada muhimmancin haɗin kai, soyayya, da ‘yan uwantaka, yana mai cewa ci gaban Najeriya ya dogara ne da inganta zaman lafiya tsakanin al’ummomi masu bambancin al’adu.

“Dole ne mu ƙarfafa ‘yan uwantaka, mu haɗa kai duk da bambance-bambancenmu, domin wannan ne kawai hanyar samun ci gaba a ƙasar nan,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga duk mazauna jihar da su yi nazari kan kyawawan halaye irin su jinƙai, soyayya, gaskiya, alheri, da yafiya—kyawawan halaye da Annabi Yesu Almasihu ya koyar—tare da ɗaukar darussan da ke cikin wannan lokaci na biki.

Yusuf ya kuma yi kyautar Naira miliyan 20 ga wasu kungiyoyin Kiristoci don shagulgulan bikin Kirsimeti.





Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *