Kotu ta haramta kama mai magana da yawun gwamnan Kano bayan korafin Ganduje


Babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin hana Sufeton ‘yan Sanda (IGP), DSS, da sauran hukumomin tsaro kama Malam Sanusi Bature Dawakin-Tofa, mai magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kotun ta bayar da wannan umarnin a ranar 12 ga Disamba, 2024, wanda ke kare Dawakin-Tofa daga “kame ko tsarewa, da tsoratarwa” daga IGP, DSS, da sauran hukumomin tsaro.

An kuma fadada wannan umarni zuwa ga mataimakin Sufeton ‘yan Sanda (AIG) na zone 1, kwamishinan ‘yan sanda na Kano, SP Mojirade Obisiji, DCP Akin Fakorede, hukumar tsaro ta NSCDC da sauransu.

Wannan kariya ta shari’a ta biyo bayan zargin da Dr Abdullahi Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya yi cewa Dawakin-Tofa shi ne ya kitsa dakatar da shi a matakin mazabar APC watanni shida da suka wuce.

Rikicin ya fara ne bayan Ganduje ya yi zargin cewa akwai wani tuggu da Dawakin-Tofa, wanda suke mazaba daya, da kuma gwamnatin juhar Kano karkashin jagorancin NNPP suka kitsa.

Ganduje ya bayyana cewa wannan mataki na dakatar da shi wani yunkuri ne na rage tasirinsa a siyasa.

Biyo bayan korafin Ganduje, IGP ya gayyaci Dawakin-Tofa zuwa Abuja tare da shugabannin mazabar APC na Ganduje, inda aka yi masa zargin kulla tuggu da aikata abubuwan da ka iya haddasa rashin zaman lafiya.

Wannan rikici, wanda ya samo asali daga takaddamar siyasa tsakanin manyan jiga-jigan siyasar Kano guda biyu, ya kara ta’azzara dangantakar da ke tsakanin Ganduje da gwamna Yusuf.

Dawakin-Tofa, ta bakin lauyoyinsa karkashin jagorancin Barr. Haruna Musa Muhammad, ya kalubalanci wannan gayyata ta hanyar kai kara gaban kotu, yana mai bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na siyasa don bata masa suna da kuma hana shi gudanar da aikinsa.





Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *