Majalisar dokokin Kano ta amince da nadin sabbin kwamishinoni 7


Majalisar dokokin Kano ta amince da mutane bakwai da gwamna Abba Kabir Yusif ya aike domin tantancewa ya nada su a matsayin kwamishinoni Kuma ‘yan majalisar zartarwar jihar nan.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala tantance mutanen bakwai.

A cewar Dala dukkanin wadanda gwamnan ya turo majalisar nagartattu ne Kuma masu kishi da San cigaban Kano.

Dala ya Kara da cewar tantancewar tasu ta mayar hankali ne bangaren da kowanne su yake da kwarewa.

Majalisar tace a yau zata aikewa gwamna Abba Kabir Yusif da rahoton ta domin bashi damar rantsar da su da Kuma tura su ma’aikatun da zasu yi aiki.





Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *