Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Kwara ya rasu


Tsohon kwamishinan yada labarai a jihar Kwara, Alhaji Abdulrahim Adisa, ya rasu a safiyar Alhamis yana da shekaru 91.

A cewar wata sanarwa daga Sakataran kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), Olayinka Alaya, an gudanar da sallar jana’iza rsa da misalin karfe 10:00 na safe a Makabartar Musulmai ta Osere, Ilorin, babban birnin jihar.

Alhaji Adisa ya taba rike mukamin babban Manajan jaridar gwamnatin jiha mai suna Herald Newspapers, Kwamishinan yada labarai da kuma Shugaban karamar hukumar Moro a jihar.

A cikin sakon ta’aziyya da ya aike ta hannun Babban Sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye, Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya tuna da gagarumar gudummawar Alhaji Adisa ga harkar jarida, musamman a matsayin tsohon ma’aikacin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

Gwamna Abdulrazaq ya nuna jimaminsa ga ‘yan jarida a jihar, musamman ma’aikatan Herald, tare da iyalan Alhaji Adisa.

Ya roki Allah ya bai wa Alhaji Adisa Aljannah Firdausi kuma ya bai wa iyalansa hakurin jure rashin.





Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *